BBC navigation

'An aikata cin hanci a tsohuwar gwamnatin Brazil'

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 11:09 GMT

Shugaban kasar Brazil Da Silva sa kuma Jose Dirceu

Kotun Koli a kasar Brazil ta sami wani babban na hannun damar tsohon Shugaban kasar Luiz Lula Da Silva da laifin cin hanci.

Jose Dircue wanda shi ne Shugaban ma'aikata na fadar gwamnatin kasar a tsakanin Shekara ta dubu biyu da uku zuwa dubu biyu da biyar an zarge shi ne da laifin bullo da wani shiri wanda ya rinka amfani da kudaden gwamnati don ba da toshiya ga jam'iyyun adawa da nufin neman goyon bayansu a majalisar dokoki.

Jose Dircue ya musanta zargin amma fa idan aka yanke masa hukuncin laifin zai iya kasancewa a gidan yari daga shekaru biyu zuwa goma sha biyu.

Shariar dai za ta zama wata magwajin yaki da cin hanci a tarihin gwamnatin Luiz Da Silva.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.