BBC navigation

Dalibai sun yi zanga-zanga a Patakwal

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:43 GMT

Patakwal a Najeriya

Daliban Jami'ar Patakwal sun gudanar da zanga-zanga don nuna bacin-ransu ga kisan da wasu samari suka yi wa wasu dalibai.

Zanga-zangar wadda ta kai ga kone kone ta sa an rufe Jamiar har sai illa ma sha Allahu.

Ana zargin wasu samari a Al'ummar Aluu kauyen da yake kusa da Jamiar da kashe wasu dalibai hudu gami da kona su da tayoyi saboda suna zargin su da satar naura mai kwakwalwa da kuam wayar salula.

A makon da ya gabata ma dai an kashe wasu dalibai a makarantar koyon Fasaha ta Tarayya dake Mubi a Jihar Adamawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.