BBC navigation

An rufe jami'ar Patakwal saboda tashin hankali

An sabunta: 10 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 11:54 GMT

Patakwal a Najeriya

An rufe jami'ar Patakwal a Najeriya sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar da aka yi bisa kisan wasu dalibai hudu da aka zarga da satar wayoyin salula da kwamfiyutar hannu.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafin internet na You Tube ya nuna yadda aka yi wa daliban kisan kiyashi.

Dalibai sun ce an kashe mutanen hudu ne bayan da aka yi musu kallon barayi bisa kuskure a kauyen Aluu da ke kusa da garin Patakwal mai arzikin man fetur.

Mahukuntan jami'air sun umarci dalibai su tafi gida bayan da zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali, inda aka kona gidaje, da shaguna da motoci.

Masu aiko da rahotannin sun ce an baza jami'an tsaro masu kwantar da tarzoma a jami'ar, kuma mahukunta sun ce za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai al'amura sun daidaita.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.