BBC navigation

Shell na fuskantar shari'a kan aikinsa a Najeriya

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:17 GMT
Malalar mai a yankin Niger Delta a Najeriya

An dade ana samun malalar mai a yankin Nigerb Delta mai arzikin man fetur a Najeriya

Wakilan kamfanin mai na Shell na gurfana a gaban kotu a Holland domin fuskantar zargin gurbata wasu kauyuka da dama a yankin Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya.

Wasu manoma hudu ne 'yan Najeriya da reshen kungiyar kare muhalli ta Friends of the Earth a Holland, suka shigar da karar.

Idan har suka samu nasara, to hakan zai bude kafa ga bukatun neman biyan diyya, a cewar wakiliyar BBC Anna Holligan wacce ke halattar zaman kotun.

Kamfanin Shell dai ya ce bai samu damar share dukkan man da ya malala ba saboda rashin tsaro.

Katafaren kamfanin mallakar kasashen Ingila da Holland, ya ce fiye da rabin malalar man da ake samu a yankin Niger Delta, na faruwa ne sakamakon satar mai da ayyukan masu zagon kasa.

Manoman da suka shigar da karar na neman alkalan kotun da su tilastawa Shell din ya biyasu diyyar asarar da su kai ta fuskar tattalin arziki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.