BBC navigation

Ranar Alhamis ce ranar yara mata ta duniya

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:37 GMT
Yara mata 'yan makaranta a kasar Pakistan

Yara mata 'yan makaranta a kasar Pakistan

Ranar Alhamis 11 ga watan Octoba ce ranar yara mata ta duniya ta farko da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe da nufin jawo hankalin kasashen duniya.

Haka kuma domin yin waiwaye kan halin da yara mata ke ciki.

A ranar ne kuma ake sa ran Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar dinkin duniya UNICEF, zai kaddamar da wani rahoto game da aurad da yara mata da basu kai munzali ba.

Kungiyoyin yara mata ne da tallafin gwamnatocin wasu kasashe suka yi kamun kafa da kuma matsin lamba ga Majalisar domin ta rika kebe rana guda a duk shekara don tunawa da yara matan, inda a bana ake maida hankali ga kyautata hakkokin yara matan.

Yara mata a kasashe masu tasowa kamar Najeriya dai na fama da matsalolin rayuwa da dama, kama daga yawan fyade daga manya, zuwa fatauci da kuma safararsu musamman a kudancin kasar.

Bayanai dai na nuni da cewa dubun-dubatan yara mata ne 'yan Najeriya kan tsinci kansu cikin irin wannan yanayi wasu lokutan ba tare da sanin iyayensu ba.

To sai dai kuma duk da irin wadannnan matsaloli da yara mata ke fuskanta, bayanai na nuni da cewa cikin 'yan shekarun nan, ana samun karuwar adadin yara matan dake shiga sana'o'in hannu na neman halaliya.

Haka kuma ana samun karwar yara matan da ke zuwa makarantu kama daga firamare zuwa sakandare har ma da jami'a, ko dayake dai har yanzu takwarorinsu yara maza na gaba da su nesa ba kusa ba ta wannan fuska.

Har yanzu akwai dimbin yara mata da basa zuwa makaranta musamman na boko, musamman a jihohi na arewacin Najeriyar saboda dalilan da ake ganin sun hada da talauci da al'ada da kuma sakaci baki daya da harkar ilimin daga bangaren masu ruwa da tsaki.

Masu lura da al'amura dai na ganin inganta yanayin rayuwar iyaye da kara fadakarwa, da kuma sanya yara matan kan turba madaidaciya, za su taimaka gaya wajen kubutar da yara mata daga dimbin matsalolin da suke fuskanta da kuma kara armashi ga irin nasarori da cigaba da wasunsu ke samu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.