BBC navigation

Asibitin birnin Aleppo ya sha lugudan wuta

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:23 GMT
Asibitin birniin Aleppo na kasar Syria

Asibitin birniin Aleppo na kasar Syria

Likitoci a wani asibiti a birnin Aleppo da ke Syria sun ce jiragen saman yakin gwamnati sun yi barin bama-bamai da gangan a kan asibitin akalla har sau goma sha biyu, sannan kuma ya sha yin luguden wuta da makaman igwa.

Wakilin BBC da ya ziyarci asibitin na Aleppo ya ce an yi kacakaca da benayen da ke can saman benen asibitin, kana a dakunan dake kasan ginin akwai abubuwa marasa kyawun gani yayinda likitoci da nas-nas da ma masu aikin sa-kai kalilan din da suka saura ke fafutukar kula da marasa lafiya fiye da dari a kullum.

Galibi dai marasa lafiyar da daidaikun likitoci, ma'aikatan jinya da masu aikin sa kan da suke taimakawa na fama da munanan raunukan da suka samu ne sakamakon harin bom din.

Daya daga cikin likitocin da ke asibitin na birnin Aleppo ya bayyana damuwarsa da cewa ''Mun rasa komai, mun rasa kasarmu, mun rasa kwanciyar hankali, mun kuma rasa abokanmu; mutane fiya da dubu talatin.''

Bayan da ya ganewa idanunsa yadda lamarin yake, da ma halin da marasa lafiya da likitoci da ma'aikatan jinya ke ciki, wakilin BBC Ian Panell ya ce, akwai gine-gine da dama da suka lalace sakamakon harin bom din, da galibi jama'a ke cewa an kai shi ne da gangan, kana ga yara na ta kuka, yayinda iyayensu suka shiga wani hali daga irin raunukan da suka samu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.