BBC navigation

EFCC a Najeriya ta bankado almundahanar miliyoyin Nairori

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:36 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya wato EFCC, ta ce ta bankado wata almundahana ta kusan naira miliyan dubu ashirin da ake zargin an tafka a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Imo, Cif Ikedi Ohakim.

Wannan bincike dai wani ci gaba ne na jerin binciken da hukumar ta EFCC ke gudanarwa shekara da shekaru a kan wasu tsofaffin gwamnonin jihohin kasar, wadanda suka hada da na Abia da Enugu da Ebonyi da Borno da Jigawa da Zamfara da dai sauransu.

Batun tuhumar wasu tsofaffin gwamnoni a Najeriya da ake zargi da tafka almundahana da kudaden gwamnati lokacin da suke kan mulki, wani abu ne da jama'a da dama ke ganin har yanzu hukumar ta EFCC ta kasa tabuka komai wajen hukunta su, hakan ne ma yasa wasu ke ganin abu ne mai kamar da wuya a irin ikirarin da hukumomin ke yi na yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Sai dai a koda yaushe ita hukumar ta EFCC kan ce ita dai babban aikinta shi ne gudanar da bincike kan laifuffukan da suka shafi tattalin arziki da kudade ne, inda da zarar sun kammala bincike tare da hujja su kan gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.