BBC navigation

"Tarayyar Turai ta cancanci yabo" - Inji Ms Merkel

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:56 GMT
Tutar Tarayyar Turai

Tutar Tarayyar Turai

Kwamitin kyautar Nobel ya bada kyautar Nobel din zaman lafiya ta bana ga tarayyar turai.

Shugaban Kwamitin yace a shekaru shidan da suka gabata, tarayar turai ta bada gudummuwa wajen cigaban sasantawa da damukradiya da kuma 'yancin dan Adam

Kwamitin yace Tarayyar Turai ta taimaka wajen sake gina turai bayan yakin duniya na biyu, ya kuma jinjina mata saboda rawar da ta taka bayan faduwar bangon Berlin a shekarar 1989

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace kyautar, wata tunatarwa ce dake nuna kada a mance da darussan da aka koya a tarihi.

Da wannan sanarwa ce aka bada kyuatar Nobel ta zaman lafiya ta bana ga Kungiyar Tarayyar Turai.


A sakamakon hakan, kwamitin bada kyautar Nobel na kasar Norway ya nuna gamsuwa kenan da matakan da tarayar Turai take dauka a matsayin kungiyar tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.


Kwamitin ya ce ya baiwa kungiyar wannan kyauta ce domin yabawa da shekaru sama da sittin da ta kwashe tana bada gudunmawa wajen sasanta tsakanin al'umma da yada dimokradiyya da kuma kare hakin bil'adama.

Shugaban hukumar gudanarwar tarayyar Turan Jose Maneul Barroso ya mika godiya ga kwamitin kan wannan kyauta:


Ya ce, wannan ba karamar karramawa ba ce ga tarayyar Turai da , da kwamitin kyuatar bada kyuatar Nobel na Norway ya bata kyautar Nobel ta zaman lafiya ta 2012.

Wannan babu shakka wani karimci ne ga mutane miliyan dari biyar 'yan kasashen turai, da kuma dukkan kasashe mambobin dukan wasu cibiyoyi na kasashen Turai.

Ta wani bangare an kafa kungiyar ce, a sakamakon bukatar da ake da ita ta kauce ma tafka fada tsakanin kasashe mambobinta.


Ana nuna cewar fadada kungiyar da aka yi ta kunshi kasashen gabashin Turai ya sa da wuya nan gaba a sake samun wani rikici kwatankwacin wanda aka yi a tsohuwar kasar Yugoslavia.


Sai dai kuma wasu na iya cewa baiwa kungiyar ta tarayar Turai irin wannan kyauta a daidai wannan lokaci da kungiyar ke ta fadi tashi na magance matsalar tattalin arzikin da ta dabaibaye ta, abu ne da bai dace ba.


Mutane a kasashe irin su Girka da Ireland da kuma Portugal zasu iya yi ma kungiyar tarayyar Turan kallon wadda ke tilasta sa kasashe daukar matakan tsuke bakin aljihu, kafin ta bada tallafin kudi, maimakon wadda ke tabbatar da zaman lafiya.


Wannan shawara ta kwamitin bada kyautar Nobel na janyo kacenace a ita kanta kasar ta Norway, kasar da a baya sau biyu tana kin amince wa da tayin da aka yi ma ta na shiga cikin kungiyar.


Masu suka na cewa shawara bada kyuatar ta kasance mai daure kai, suna masu cewa a yanzu kungiyar ta tarayyar Turai yamutsi ta ke janyowa maimakon zaman lafiya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.