BBC navigation

'Yan takarar mataimakin shugaban Amurka sun tafka muhawara

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 11:58 GMT
'Yan takarar mataimakin shugaban kasar Amurka

'Yan takarar mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden da Paul Ryan.

'Yan takarar mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden da Paul Ryan sun yi arangama a zazzafar muhawarar da aka tafka a daren Alhamis, yayinda ake shirin tunkarar zaben shugaban kasa a watan Nuwamba mai zuwa.

Mr Biden, na Jam'iyar Democrat, ya kasance cikin fushi, yana mai katse hanzarin abokin fafatawar ta sa yayin da yake kare shugaba Barack Obama.

Mr Ryan, na Jam'iyar Republican kuwa ya kasance cikin natsuwa ne a muhawarar sa ta farko da aka yada a kafar gidan talabijin na kasar.

Manufofin hulda da kasashen waje da kuma tattalin arzikin cikin gida ne batutuwan da suka kankane muhawara daya tilo da aka yada ta gidajen talabijin tsakanin 'yan takarar mataimakin shugaban kasar Amurka, wato mataimakin shugaban kasa mai ci Joe Biden na Jam'iyyar Democrat da dan majalisar dokoki Paul Ryan na Jam'iyyar Republican.
Mista Ryan ya ce matsayin da Amurka ta dauka. a kan Iran da Syria ya nuna iyakar manufofin hulda da kasashen waje na gwamnatin Obama, zargin da Mista Biden ya ce ba shi da tushe balle makama.

Sai dai batu a kan haraji ne ya fi daukar hankali a muhawarar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.