BBC navigation

BBC za ta kaddamar da bincike kan wani tsohon ma'aikacinta

An sabunta: 13 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:07 GMT
Fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a BBC Jimmy Savile

Fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a BBC Jimmy Savile

BBC za ta kaddamar da bincike na cikin gida har kashi biyu a kan zarge-zargen da ake yi wa daya daga cikin fitattun masu gabatar da shirye-shiryenta, Jimmy Savile, cewa ya yi lalata da kananan yara mata masu dimbin yawa a cikin shekaru da dama - wani lokaci ma a cikin gine-ginen tashar ta BBC.

Darakta Janar na BBC, George Entwistle, ya ce ba za a sake nazari nan take ba a kan shawarar da wani shirin tashar ya yanke ta dakatar da binciken da ya shirya yi a kan Savile, wanda ya mutu bara.

BBC dai ta ce daga bisani za a gudanar da wani nazarin, wanda zai binciki ko yanayin aiki a tashar ta BBC ya ba da damar aikata irin wannan ta'asa, amma sai bayan 'yan sanda sun kammala binciken da suke yi a kan zarge-zargen.
Bincike na farko dai za a fara ne kai tsaye kan ko me ya sa aka jingine binciken game da Mista Savile a bara.

Sauran biyun kuma kan ko wata al'ada ce a BBC a wannan zamanin ta baiwa Savile din damar aikata cin zarafi da lalata da kananan yara.

'Yan sanda dai sun ce yanzu haka sun samu hanyoyin bincike kimanin 340.

A wani taron manema labarai, Darakta Janar na BBC, George Entwistle ya ce kwararru kan bincike masu zaman kansu wadanda za a bayyana sunayensu a mako mai zuwa ne za su jagoranci dukkannin binciken biyu da hukumar gudanarwar BBC ta bayar, yana kuma mai neman afuwar matan da al'amarin ya shafa a madadin BBC.

Ya ce ''wadanda cin zarafin Jimmy Savile ya shafa sun fuskanci damuwa a cikin shekaru, kuma ya zama wani hakkin mu da na masu sauraren mu ya rataya a wuyanmu na su fahimci abinda ya faru tare da tabbatar da cewa wani abu mai kama da haka bai sake faruwa ba.''

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.