BBC navigation

Brahimi zai gana da jami'an kasar Turkiyya

An sabunta: 13 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:48 GMT
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Lakhdar Brahimi

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Lakhdar Brahimi

Wakilin kasashen Larabawa da Majalisar Dinkin Duniya a kan rikicin kasar Syria, Lakhdar Brahimi, zai gana da jami'an kasar Turkiyya a Istanbul, a daidai lokacin da kasar ta Turkiyya ta kara tsunduma cikin rikicin kasar Syria.

Mista Brahimi dai, wanda bai jima da kammala ziyara a Saudi Arabia ba, ba shi da wani takamaiman shirin samar da zaman lafiya; don haka zai ji ta bakin Turkiyya ne a kan rikicin na Syria.

'Yan kasar Turkiyya biyar ne dai suka rasa rayukansu a luguden wutar da dakarun Syria suka yi a ketaren iyaka a wannan watan, ranar Laraba kuma Turkiyya ta karkata akalar wani jirgin saman fasinja na Syria wanda ta ce yana dauke da kayan soji.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.