BBC navigation

Shugaba Morsi ya yi amai ya lashe.

An sabunta: 13 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:44 GMT
shugaba Muhammad Morsi na Masar

shugaba Muhammad Morsi na Masar

Shugaban Masar, Muhammad Morsi ya janye kurarin da yayi a wata takaddama tsakaninsa da babban mai gabatar da kara na kasar, inda ya kyale shi ya ci gaba da rike mukaminsa, bayan tun da farko ya bada sanarwar korarsa.

An bada sanarwar hakan ne bayan wata ganawa tsakanin mai gabatar da karar, Abdul Majid Mahmoud da shugaba Morsi.

Kafin haka dai, babban mai shigar da karar ya koma bakin aiki cikin tsauraran matakan tsaro.

Ranar Alhamis ne dai shugaba Muhammad Morsi yayi yunkurin sauke babban mai shigar kara na kasar bayan ya wanke wasu makusantan tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak su sama da arba'in, daga zargin kitsa hare-haren da aka kaiwa masu zanga-zanga bara.

Wakilin BBC ya ce matakin da babban mai shigar da karan ya dauka na komawa bakin aiki duk da umurnin ya sauka daga kan mukaminsa, ya kunyata shugaban kasar.

Mataimakin mai gabatar da karar, ya ce rikicin ya taso ne kan mutumin da shugaban kasar ya zaba domin nadawa jakadan Masar a Vatican .

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.