BBC navigation

An kai shugaban kasar Mauritania jinya Faransa

An sabunta: 14 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:14 GMT

Muhammed Abdul azeez, shugaban kasar Mauritania

An kai shugaban Mauritania, Mohammed Ould Abdul Aziz zuwa Faransa domin duba lafiyarsa saboda raunukan da ya samu sakamakon harbin bindiga.

Da yake jawabi ta gidan talabijin na kasar, Ministan Sadarwa, Hamdi Ould Mahjoub, ya ce rayuwar shugaban kasar, wanda aka kwantar da shi a asibiti ana yi masa magani saboda raunin da ya yi a dantse, ba ta cikin hadari.

Ministan ya kuma ce wata tawagar sojoji 'yan sintiri ce ta bude wuta bisa kuskure a kan ayarin shugaban kasar yayin da yake komawa babban birnin kasar, Nouakchott.

A shekarar 2009 aka zabi Janar Abdel Aziz, wanda kasashen yamma ke yiwa kallon tarnaki ga masu kaifin kishin Islama a yankin, shekara guda bayan ya jagoranci wani juyin mulki.

Rahotanni sun ce jami'an tsaro sun killace asibitin da ake yi wa shugaban kasar magani.

Kasashen yammacin duniya dai na kallon shugaba Abdelaziz a matsayin mai yin garkuwa tare da adawa da masu kaifin ra'ayin addinin Islama a yankin, musamman ma a makwabciyarta kasar Mali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.