BBC navigation

Syria na amfani da bama-bamai masu 'ya'ya kan fararen hula- Human Rights Watch

An sabunta: 14 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:05 GMT
Birnin Homs na kasar Syria

Birnin Homs na kasar Syria

Kungiyar kare hakkin biladama ta Human Rights Watch, ta zargi kasar Syria cewa amfani da nau'in bom mai 'ya'ya, wanda in ya fashe ya kan watsa kananan bama-bamai da ake kira ''Cluster Bombs'' kan fararen hula yana karuwa.

Kungiyar ta ce ta kalli faifan bidiyon da aka saka a shafin yanar gizo da ke nuna hare-haren da aka kai ta hanyar amfani da irin wadannan nau'in bama-bamai a cikin makonnin da suka gabata.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta kara da cewa faya-fayen bidiyon sun nuna cewa dakarun gwamnatin na amfani da makaman da aka kera a kasar Rasha.

Kasar Syria dai bata shiga jerin kasashe darin da suka rattaba hannun yarjejeniyar hana amfani ko hada nau'in bama-baman masu rassa ba, da aka bayyana cewa ko wane bom guda na kunshe da akalla kananan bama-bamai ar'ba'in.

A cikin watan Yulin da ya gabata, kungiyar ta Human Rights Watch ta ce ta tattara wasu bayanai da ba a tabbatar da su ba game da amfani da dakarun kasar Syriyar ke yi da irin wadannan nau'in bama bamai, amma kuma ta ce a cikin 'yan kwanakin nan adadin yawan hare-haren da suke kaiwa da bama-baman masu rassa da ke dauke a cikin faifan bidiyon a shafin internet na kara karuwa.

Nau'in bama-baman masu watsuwa da aka fara kerawa tun lokacin yakin duniya na biyu, akan sake su ne ta sama, kana kananan bama-baman dake kunshe za su ci gaba da haddasa munanan raunuka da mutuwar mutane har na tsawon shekaru da dama.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.