BBC navigation

Syria ta saka takunkumi kan jiragen fasinjan kasar Turkiyya

An sabunta: 14 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:26 GMT
Jirgin kasar Turkiyya

Jirgin saman kasar Turkiyya

Kamfanin dillancin labaran Syria ya ce gwamnatin kasar ta saka takunkumin hana duk wani jirgin fasinjan kasar Turkiyya bi ta sararin samaniyarta.

Matakin na zuwa ne bayan da kasar Turkiyyar ta kama wani jirgin kasar Syria a ranar Laraba, bayan tasowarsa daga birnin Moscow, inda ta ce ta kwace wasu kayayyakin yaki na gwamnatin Syria.

A baya-bayan nan dai Fira Ministan Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi suka kan abinda ya kira gazawar Majalisar Dinkin Duniya wajen dakatar da kashe-kashen dake faruwa a kasar Syria.

Wannan mataki da kasar Syriyar ta dauka ya nuna kararara irin takaddama da takun sakar dake ci gaba da wanzuwa tsakanin ta da kasar Turkiyya.

Fira Ministan kasar ta Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, yayi kakkausar suka ne ga ita kan ta Majalisar Dinkin Duniya kan abinda ya ce na jan kafa game da rikicin da ke ci gaba da faruwa a kasar Syria, inda ya ce gazawar da Majalisar Dinkin Duniyar ta yi wajen warware matsalar zub da jinin dake faruwa a Syriyar ya baiwa shugaba Bashar al-Assad wata damar kashe daruruwan fararen hula a kullum.

Mr Erdogan kuma yayi kakkausar suka kan kasashen Rasha da China da cewa suna marawa kasar Syria baya ta fuskar diplomasiyya.

A baya dai Mr Erdogan din yayi kiran da a kawo sauye-sauye a bangaren Majalisar tsaron kasar ta Syria, inda kasashen Rasha da China suka hau kujerar na ki game da yanke shawara kan kasar ta Syria.

Ta wani gefen kuma, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Lakhdar Brahimi ya yi wata ganawa da Minsitan harkokin wajen kasar Turkiyya Ahmet Davutoglu a birnin Istanbul, sai dai ba a samu wasu bayanai ba game ganawar ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.