BBC navigation

Tsohon sarkin Cambodia Sihanouk ya mutu

An sabunta: 15 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:08 GMT

tsohon sarkin cambodia Sihanouk


Tsohon Sarkin kasar Cambodia, Norodom Sihanouk, ya rasu a kasar China bayan da yayi fama da rashin lafiya.

Norodom Sihanouk, mai shekaru tamanin da tara, ya taka muhimmiyar rawa a tarihin kasar Cambodia cikin fiye da shekaru sittin inda kasar ta yi fama da yake-yake da Amurka a Vietnam da kuma kisan kiyashi a lokacin mulkin Kahmer Rouge.

Tsohon Sarkin da kasar Faransa ta nada shi a shekarar alif dari tara da arba'in da daya ya jagoranci kasar har ta kaiga samun 'yancin kai a shekarar alif dari tara da hamsin da uku.

Tsohon shugaban yanada martaba a idanun yan Cambodia amma kasashen waje na yi masa kallon wani mai mulkin kama karya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.