BBC navigation

Pursunoni sun tsere a Libya

An sabunta: 15 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:11 GMT
Jami'an tsaron Libya

Jami'an tsaron Libya

Rahotanni daga Libya sun ce kimanin fursunoni 120 sun tsere daga wani gidan bursuna dake Tripoli, babban birnin kasar.


An ruwaito shugaban dogarawan tsaron kasar, Khaled al-Sharif, yana cewa jami'an tsaro na zaman ko-ta-kwana, domin su kamo su, bayan da suka gudu daga gidan bursunan Al-Jadaida.

Yace tuni har an kama wasunsu.


Hukumomin Libyan sun sake kwace gidajen yari da dama, wadanda suka hada harda na Al-Jadaidan, wadanda a da suke hannun tsaffin 'yan tawayen da suka yaki Colonel Gaddafi a bara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.