BBC navigation

Za a kai Malala Yusufzai Birtaniya neman magani

An sabunta: 15 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:20 GMT

Malala yousafzai

Za'a kai karamar yarinyar nan 'yar kasar Pakistan, Malala Yusufzai da 'yan kungiyar Taliban suka harbe ta a kai saboda gangamin data ke yi kan ilimin 'ya'ya mata zuwa Birtaniya don yi mata magani.

Wani gidan talbijin na kasar Pakistan ya ce gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ita ta dauki nauyin kula da yarinyar inda tuni aka yi shatan wani jirgi da zai daukota zuwa Birtaniya.

Ita dai Malala Yusufzai na kan hanyarta ta komawa gida ne daga makaranta lokacin da wani dan bindiga ya harbe ta a kai a makon jiya.

Ko shakka babu 'yan Taliban na jin haushin fafutukar da 'yarinyar ke yi a kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.