BBC navigation

Tsohon Shugaban Bosnia ya fara kare kansa

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:58 GMT
Radovan Karadzic

Radovan Karadzic

Tsohon shugaban Sabiyawan Bosnia Radovan Karadvzic ya soma kare kansa a gaban kotun hukunta laifukan yaki dake birnin Hague ne, ta hanyar shafe mintuna 90 yana bada bayanai akan irin yadda ya fahimci abinda ya janyo yakin Bosnia da kuma yadda lamarin ya cakude.

Ya bayyana kansa a matsayin mutum mai son zaman lafiya da kuma saukin kai.

Sai dai kuma shine mutumin da ake zarginsa da aikata kisan kiyashi a lokacin da yakin ya barke a Yugaslavia.

Radovan Karadzic ya kuma ce karya ce tsagwaro aka yi masa akan zargin duk ta'asar da aka ce ya tafka, a cewarsa kafafen yada labarai na kasashen wajen ne suka kitsa batun .

Daga cikin zarge zargen da ake yiwa Karadzic hadda laifin kashe musulmai fiye da 7000 a Srebrenica da kuma karin wasu mutane 10000 wadanda suka mutu a cikin watanni 44 da aka shafe ana rikici a Sarajevo.

Tuni dai aka yankewa wasu daga cikin makarabban Karadvzic hukuncin daurin shekaru masu yawa, amma kuma a wannan sharia'ar da ake masa, yana da damar kiran shaidu akalla dari don su goyi bayansa abinda ke nuna cewar wannan shariar za a shafe shekaru ana ayi ba tare da yanke hukunci ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.