BBC navigation

JTF ta ce ta kashe 'yan Boko Haram su 24

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:14 GMT
Jami'an tsaron Nijeriya

Jami'an tsaron Nijeriya

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa JTF a Maiduguri dake arewacin Najeriya ta ce, ta kashe mutane ashirin da hudu da ta ke zargin 'yan kungiyar nan ce da ke kira da sunan Boko Haram a wata arangama.

Rundunar tsaro ta JTF ta ce, 'yan kungiyar Boko Haram din sun kai hare-hare ne a sansanonin soja dake Maidugurin:

Wakilin BBC ya ce a farkon wannan watan ne dai rundunar sojan Najeriya ta musanta kashe fararen hula yayin farmakin da suka kai a wata mafakar 'yan kungiyar da ke birnin.

Dakarun tsaro dai sun killace manyan tituna dake birnin na Maiduguri bayan jerin fashe-fashen bama-bamai da kuma karar harbin bindiga tun daga cikin daren jiya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.