BBC navigation

Wasu abubuwa masu kara sun fashe a Maiduguri

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:11 GMT

bam a Najeriya

A Najeriya, an ji karar wasu abubuwa masu fashewa da kuma karar harbe harben bindigogi a daren jiya a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar.

Rahotanni sun ce wasu yan bindiga sun harbe wani mai bada hannu kan titi a jiya.

A 'yan kwanakin nan dai sha'anin tsaro ya kara tabarbarewa a birnin Maiduguri inda ake samun rahotanni harbe harbe da tada bama bamai.

Birnin Maiduguri dai na fama da artabu tsakanin yan kungiyar Ahlulsunna lilda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko haram da kuma Jamian tsaro.

Ko a ranar Lahadin da ta gabata wasu yan bindiga sun harbe mutane hudu ciki har da wani mai sarautar gargajiya.

Ko da yake harin na yammacin jiyan babu wanda ya dauki alhakkin kaiwa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.