BBC navigation

Tarihin Mitt Romney

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:14 GMT
Mitt Romney

Mitt Romney na fatan amfani da kwarewarsa a fannin kasuwanci wurin nuna cewa shi ne zai iya farfado da tattalin arzikin Amurka

Mitt Romney ya shiga takarar White House ne ta 2012 a matsayin wanda akewa kallon zai iya kai labari. Kuma ya ci gaba a haka har lokacin da ragowar suka mika masa wuya.

Mr Romney, wanda tsohon gwamnan jihar Massachusetts ne, yana da arziki da kuma kwarewa ta fannin kasuwanci.

Sananne ne a Amurka kuma yana da abokai masu bashi gudummawar kudi da magoya bayan da ya tara tun lokacin da ya fito takar shugaban kasa a karon farko a 2008 wacce bai yi nasara ba.

Yana da kwarjini matuka, kuma yana tare da matarsa Ann Romney tun bayan da suka yi aure fiye da shekaru arba'ain da suka gabata.

Mr Romney ya sha kayi a hannun Senator John McCain na jihar Arizona a 2008, sai dai bai yi kasa a gwiwa ba.

Jim kadan bayan rantsar da shugaba Obama, sai ya ci gaba da yunkurinsa na neman goyon baya domin shekara ta 2012.

Mitt Romney

Dan takar Jam'iyyar Republican

An haifi Willard Mitt Romney a 1947 a Michigan

Mahaifinsa George Romney ya taba zamo gwamnan Michigan

Ya halarci jami'ar Brigham Young da Harvard

Ya zamo shugaban kamfanin Bain Consulting

Shi ya jagoranci shirya gasar wasannin Olympics a Salt Lake City

Ya zamo gwamnan Massachusetts a shekara ta 2002

Romney ya zamo dan takarar Republican a Agusta 2012

Fatansa shi ne kwarewarsa a fannin kasuwanci za ta taimaka masa wurin shawo kan masu kada kuri'a cewar shi ne ya fi cancanta ya farfado da tattalin arzikin Amurka fiye da shugaba Obama.

Bain Capital

An haifi Willard Mitt Romney a 1947 a Michigan.

Mahaifinsa George Romney, ya zamo gwamnan jihar daga bisani a karkashin jam'iyyar Republican, sannan ya nemi jam'iyyar ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a 1968.

Mitt Romney ya shafe shekaru biyu a majami'ar Mormon missionary a Faransa, daga nan kuma ya halarci jami'ar Brigham Young University sannan ya karanci shari'a da harkokin kasuwanci a Harvard.

Daga bisani Mr Romeny ya samu babban mukami a majami'ar ta Mormom sannan ya koma kamfanin Boston management consulting Bain and Company, inda har ya zamo shugaban kamfanin.

Shi ne kuma ya kafa kamfanin Bain Capital, wanda shi ma ke da alaka da kamfanin na Bain.

A shekarar 1994, Mr Romney ya yi kokarin kawar da kwararran dan siyasar Democrat Senator Ted Kennedy. Duk da cewa bai yi nasara ba amma ya daukaka matsayinsa a jihar da kuma wurin 'yan Republican baki daya.

An zabi Mr Romney ya zamo dan takarar jam'iyyar Republican a babban taron jam'iyyar a Tampa, Florida a ranar 28 ga watan Agusta.

Zai fafata da Barack Obama a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.