BBC navigation

An yi zazzafar mahawara tsakanin Obama da Romney

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:07 GMT

Barack Obama da Mitt Romney


Shugaban Amurka Barrack Obama da abokin karawarsa a zaben shugabancin Amurka Mitt Romney, sun fafata a zagaye na biyu na mahawarar da suka yi, da aka watsa kai tsaye ta gidajen talbijin a dai dai lokacin da ya rage makwanni uku a gudanar da zaben shugaban kasar.

A lokacin da suka fuskanci masu kada kuri'a da ba su yanke shawarar wanda za su zaba ba, 'yan takarar biyu dai sun kalubalanci juna ne kan batutuwan da suka shafi haraji da aikin yi da kuma makamashi.

Sun kuma yi ta katse junan su inda Mr Obama ya yi ta nanata cewa abokin karawar ta sa ba ya fadin gaskiya.

Da su ka tabo batun kisan da aka yiwa Jakadan Amurka a Libya, Mr Romney ya ce wannan batun ya nuna irin rashin alkiblar shugaba Obama kan yankin gabas ta tsakiya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.