BBC navigation

Jamus na son ganin hadin kan Turai

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:24 GMT

A jajibirin taron kolin tattalin arziki na sashen Turai, Jamus ta yi kira ga kasashen Turan da su karfafa dogaro da kai ta fuskar tattalin arziki.

Wani babban mai bada shawara ga shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, yace kamata yayi kasashen Turai su dinke manufofin tattalin arzikin wuri guda.

Wakilin BBC yace su dai Jamus suna so ne a kirkiro ofishin wani kwamishina mai karfin gaske a hedikwatar kungiyar ta Tarayyar Turan, wanda zai rika tantance kasafin kudin kasashen dake amfani da kudin Euro.

Sai dai Faransa na nuna dari-dari da wannan shawara ta Jamus.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.