BBC navigation

Human Rights Watch ta zargi 'yan bindiga a Libya

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:25 GMT

Kenneth Roth Babban Daraktan Human Rights watch


Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch,ta zargi 'yan bindiga a kasar Libya da halaka magoya bayan kanar Gaddafi su fiye da sittin jim kadan bayan da aka cafke da kuma kashe tsohon shugaban kasar a shekarar da ta gabata.

Kungiyar ta ce mayakan sa kai daga Misrata sun kashe magoya bayan kanar Gaddafin ne a wani otel dake garin Sirte jim kadan bayan da aka afkawa ayarin motocin tsohon shugaban kasar.

A cewar kungiyar ta Human Rights Watch, wasu shaidu sun nuna cewa daya daga cikin 'ya'yan marigayi Gaddafin Mutassim, an kashe shi ne bayan da aka kama shi aka kai shi Misrata, inda kuma kungiyar ta yi kira ga hukumomin Libyan da su gudanar da bincike kan wannan al'amari.

Kotun laifuffuka ta duniya dai na da ikon hukunta aikata laifuffukan yaki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.