BBC navigation

'Yan sanda sun kama 'barawon' kambun sarautar Ghana

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:03 GMT
Basaraken Ashanti

Basaraken Ashanti

'Yan sandan kasar Sweden sun kama mutumin da ake zargi da sace kambun sarauta na wani basaraken Ghana a wani otel a Oslo a makon da ya gabata.

'Yan sandan sun kama mutumin ne a filin tashi da saukar jiragen sama na Stockholm a lokacin da ya ke kokarin barin kasar ta Sweden.

Ba a samu mutumin da kambun a tare da shi ba, kuma har ya zuwa yanzu ba a tantance ko dan wacce kasa ba ne.

An dai ankarar da jami'an 'yan sanda game da wanda ake zargin ya saci kambun sarautar ne saboda yana cikin tawagar da suka shiga otel din na Oslo a ranar Juma'ar da ta gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa kambun sarautar na da matukar tarihi da daraja, kuma an sace shi ne a cikin wata jaka dake cikin kayayyakin da basaraken ya je otel din da su, don halartar wani taron Kungiyar 'Yan kasuwar Norway da Afirka.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.