BBC navigation

Rundunar 'yan sandan Kano ta yi kame

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:14 GMT
Makamai

'Yan sanda sun cafke wadanda ake zargin su na kisa a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a arewacin Nigeria ta ce ta kama wasu mutane goma da ake zargi da kai wasu hare hare a birnin na Kano.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ana zargin mutanen da kashe wasu 'yan sanda da jami’an hukumar kare hadura, da ma wasu kashe kashe a wurare daban daban.

Sanarwar ta ce daya daga cikin mutanen ya mutu, yayin da kuma ake tsare da saura, ciki har da wani dan asalin kasar Sudan, Ibrahim Inusa

Rundunar 'yan Sandan Kanon ta ce Ibrahim Inusan ya shaida ma ta cewa su na da gungu na kwararru na masu shiryawa da kuma kisan jami'an tsaro da ma fararen hula a wurare daban daban, da su ka hada da ungwannin Gaida da Sheka da kuma Gwale

Rundunar 'yan sandan Kanon ta ce har yanzu ta na ci gaba da farautar masu aikata kashe kashen

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.