BBC navigation

Mutane dubu ashirin sun bace a rikicin Syria

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:04 GMT

Syria

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama a kasar Syria sun ce akalla mutane dubu ashirin da takwas ne aka nemesu aka rasa tun lokacin da aka fara zanga zangar nuna adawa da gwamnatin shugaba Bashar Al Assad kimanin shekara daya da rabi.

Kungiyoyin sun bayyana cewa suna da sunayen mutane dubu goma sha takwas da suka bace, kana kuma suna da labarin karin wasu mutane dubu goma da suma aka nemesu aka rasa.

Kungiyar Avaaz dake fafutika a shafin Internet ta ce gwamnatin Syriar na amfani da dabaru daban-daban na kawadda masu fafutika da 'yan tawaye tare kuma da razana jama'a don kwantar da adawar da ake nuna mata.

Mutane da dama sun hallaka sanadiyyar artabun da ake yi tsakanin 'yan tawaye da kuma dakarun gwamnatin Syria.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.