BBC navigation

Za a kafa hukumar sa ido a bankunan Turai

An sabunta: 19 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:07 GMT

Wadansu shugabannin hukumomin kudi na Tarayyar Turai

Shugabannin kasashen Tarayyar Turai da suka yi taro a Brussels sun amince su kafa wata hukuma wacce za ta rika sanya idanu a kan bankuna 6000 na kasashen da ke amfani da kudin euro.

Shugabannin sun bayar da sanarwar ce ranar Juma'a da safe kuma za ta fara aiki ne a shekarar 2013.

Sun ce sun yi matukar damuwa dangane da makomar kungiyar, don haka ne ma suke yin duk yadda za su iya wajen kare ta daga fuskantar karin matsaloli.

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai, Herman Van Rompoy, ne ya yi wa manema labarai karin bayani bayan taron, inda ya ce sun tattauna a kan batutuwa da dama:

''A watan Yuni mun amince mu kawar da matsalolin da suka yi wa bankuna tanarki. Kuma abu na gaggawa da muka amince da shi, shi ne mu kafa wata hukumar da za ta sanya idanu wajen ganin bankunan ba su fada cikin kangi ba; shi yasa Majalisar Tarayyar Turai ta kirawo taro domin samar da tsare-tsare na dokar da za ta kafa hukumar daga nan zuwa watan Janairun 2013.

Da zarar an amince da wadannan tsare-tsare wannan hukuma za ta fara aiki gadan-gadan.''

A cewar Mista Rompoy, Babban Bankin Tarayyar Turai zai taka muhimmiyar rawa wajen ganin hukumar ta tsaya da kafafunta.

Sai dai duk da wannan kwarin gwiwa da Rompoy ke da shi, kasashen Faransa da Jamus sun samu sabani dangane da lokacin aiwatar da shirin.

Ita dai Jamus ta ce ya kamata a yi taka-tsantsan wajen samar da hukumar ganin cewa kwamishinan Tarayyar Turai na da matukar ikon iya amincewa da kasafin kudin kasashen, yayin da a nata bangaren Faransa tana so ne a yi gaggawar samar da hukumar - wacce a cewarta za ta hada kan bankunan kasashen da ke amfani da euro.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.