BBC navigation

Ana taro game da rikicin Mali

An sabunta: 19 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:51 GMT

Sojojin Mali

Wakilan kasashe kimanin 30 ne tare da wasu kungiyoyin kasashen duniya ke hallara a Bamako babban birnin kasar Mali a ranar Juma'a don tattaunawa a kan rikicin da kasar ta tsinci kan ta a ciki.

Wakilan za su mayar da hankali ne a kan shirin Tarayyar Afrika na samar da kwanciyar hankali a Mali, wanda ya ruguje bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a farkon wannan shekarar.

Arewacin kasar dai yana karkashin ikon mayaka masu kishin Islama ne da wasu kungiyoyin, yayin da kudancin kasar ke karkashin ikon gwamnati maras karfi.

Wasu 'yan kasar dai sun yi zanga-zangar nuna kin amince da tura sojojin kasashen waje cikin kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.