BBC navigation

Za a sanyawa kungiyar M23 takunkumi

An sabunta: 20 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:03 GMT
Za a sanya wa 'yan tawayen M23 takunkumi

'Yan tawayen M23

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai sanya takunkumi a kan mambobin kungiyar sojin-sa kan nan ta M23 wadda ke tawaye a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

A cikin wata sanarwa, kwamitin ya ce takunkumin zai yi aiki ne a kan shugabannin kungiyar ta M23 da wadanda suka karya haramcin shigar da makamai cikin kasar.

Sanarwar dai ba ta ambaci sunan wadanda ke shigar da makaman ba.

Sai dai rahoton wani kwamatin kwararru da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa ya yi zargin cewa kasashen Rwanda da Uganda suna bayar da makamai ga 'yan tawayen da ke gwagwarmaya a gabashin kasar Congo.

Rwanda dai ta sha musanta cewa tana da hannu a rikicin kasar Congo, kuma ta yi watsi da rahoton kwararru na Majalisar Dinkin Duniya, inda ta ce yana cike da kura-kurai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.