BBC navigation

Mutane 33 sun mutu a wani hatsarin mota a Ogun

An sabunta: 20 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:28 GMT
Hatsarin mota a Najeriya

Wani hatsarin mota a Ogun ya yi sanadiyyar rayuka da dama

Rundunar tsaro ta 'yan sandan jihar Ogun a Najeriya, ta tabbatar da mutuwar mutane 33 a lokacin da wata babbar mota ta fada cikin wani kogi - a kan babbar hanyar Ogbere Ijebu cikin jihar Ogun.

Babban jami'in hulda da manema labarai na rundunar tsaro ta 'yan sanda a jihar Ogun Mr. Muyiwa Adejobi, ya fadawa BBC cewa kawo yanzu, ba a gano koda gawar mutum daya ba.

Mr. Muyiwa ya ce binciken farko ya nuna sitiyarin motar ne ya kubucewa direban babbar motar.

Ana dai dangantaka yawan hatsarurrukan da ake samu akan manyan titunan kasar da rashin hanyoyi masu kyau da kuma tukin ganganci daga su direbobin.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.