BBC navigation

An zargi Syria da kai harin bom a Lebanon

An sabunta: 20 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:06 GMT

Irin ta'adin da harin bom din da aka kai a Lebanon ya yi

'Yan siyasar kasar Lebanon da ke adawa da gwamnatin Syria sun dora alhakin harin bama-baman da aka kai a babban birnin kasar, Beirut kan gwamnatin Syria.

Tsohon Firayim Ministan kasar, Sa'ad Hariri, ya dora alhakin kisan da aka yi wa shugaban rundunar tsaron kasar, Wissam al-Hassan, wanda yana cikin mutane takwas din da suka mutu yayin harin na ranar Juma'a, akan shugaba Assad.

Mista al-Hassan ne ya jagoranci wani bincike da ya zargi Syria da hannu wajen kai harin bom din da ya yi sanadiyar mutuwar mahaifin Mista Hariri, watau Rafiq Hariri a shekarar 2005.

Kazalika a kwanakin baya, Mista Hassan, ya tsara yadda aka kama wani tsohon minista, wanda aka zarga da yunkurin aiwatar da shirin gwamnatin Syria na tayar da bama-bamai a Lebanon.

Gwamnatin Amurka da kuma kwamatin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Alla-wadai da hare-haren a ranar Juma'a.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.