BBC navigation

Daruruwan jama'a na tserewa garin Bani Walid na Libya

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:05 GMT
Sojoji a garin Bani Walid na Libya

Tashin hankali a garin Bani Walid

Daruruwan jama'a na tserewa daga garin Bani Walid na arewa maso yammacin Libya, a yayinda 'yan bindigar dake goyan bayan gwamnati ke ci gaba da luguden wuta da kuma kara kutsa kai cikin garin, wanda Marigayi Kanal Gaddafi yake da karfi

An dai ga ababan hawa da yawa dauke da iyalai da kayayyakinsu su na barin garin, wanda akai wa kofar rago

An ga wasu kuma su na neman sulalewa da kafafunsu

An dai kashe mutane fiye da ashirin a fadan da aka gwabza a garin Bani Walid a ranar asabar kadai

'Yan bindigar sun ce su na da niyyar kakkabe dukkanin magoya bayan Gaddafi dake cikin garin

Wani mutum da yake kan hanyar sa ta tserewa daga garin ya fadawa BBC cewar an rushe gidaje, an kuma katse layin wutar lantarki a wurare da dama a cikin garin.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.