BBC navigation

An gudanar da jana'izar Wissam Al Hassan na Labanon

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:16 GMT
Jana'izar Wissam al Hassan

Wani harin da aka kai na mota ne ya hallaka Wissam Al Hassan

An soma jana'izar babban jam'in leken asirin Labanon Wissam al Hassan a birnin Beruit karkashin tsauraran matakan tsaro

Dubun dubatar masu makoki da kuma masu zanga zanga ne suka hallara a dandalin mujahidai, inda a nanne aka binne gawar sa kusa da tsohon Fira Ministan Kasar Rafik Hariri, wanda shima wani harin bom na wata babbar mota ya hallaka a shekarar 2005

Nanne kuma aka binne babban dogarin shi marigayi Wissam al Hassan din

'Yan Labanon da dama dai na dora alhakin harin da ya kashe babban jami'in leken asirin akan Syria, kuma wakilin BBC a Beruit yace ga alamu jana'izar, zata rikide zuwa wata gagarumar zanga zangar nuna kin jinin Syrian daga baya

Tuni dai Syrian ta nesanta kanta da hannu a cikin harin

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.