BBC navigation

Ba a kama ni ba, in ji tsohon kakakin Kanal Gaddafi

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 04:22 GMT
An samu bayanai masu cin karo da juna game da kama Musa Ibrahim

Musa Ibrahim

Mai magana da yawun tsohon shugaban Libya marigayi Mo'ammar Gaddafi ya musanta zargin da gwamnatin kasar ta yi cewa ta kama shi.

A ranar Asabar ne ofishin Firayim Ministan Libya ya ce an cafke tsohon kakakin Kanal Gaddafi, kuma daya daga cikin mutanen da aka fi nema ruwa-a-jallo, Musa Ibrahim.

Sai dai daga baya kakakin Firayim Ministan Libya, Naser Al-Manaa, ya nesanta kansa daga bayanan da ke cewa an kama Musa.

Yanzu dai an sanya wata murya da aka nada a shafukan sada zumunta na intanet wacce aka ce ta Mista Musa ce inda ya musanta cewa an kama shi.

Hasalima ya ce ba ya cikin kasar.

Ya zargi gwamnatin Libya da yin karairayi domin kawar da hankulan mutane daga cin zarafin da take yi wa mutane a birnin Bani Walid da ke yammacin kasar.

Wadansu majiyoyi sun ce a can Bani Walid ma, mazuna birnin sun ce gwamnati ta yi hakan ne don kawar da hankulan mutane daga azabtarwar da take yi musu.

A makonnin da suka gabata dai, garin ya kasancewa wani fagen daga inda ake fafatawa tsakanin dakarun da gwamnatin kasar ke marawa baya da kuma mayakan da ke goyon bayan Kanal Mo'ammar Gaddafi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.