BBC navigation

An gudanar da gangamin neman rage farashin mai a Nijar

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:18 GMT
Shugaba Mahamadou Issoufu na Nijar

'Yan Nijar na neman gwamnati ta rage farashin mai

A jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun sake jaddada bukatar su ta ganin gwamnatin Kasar ta rage farashin mai a
kasar ta yadda al'amurra za su daidaita .

A cewar kungiyoyin, tsadar man ce umulhaba'isin hauhawar farashin kayayyakin masarufi da sauran abubuwan dake mayar da kasa baya.

Kungiyoyin dai sun yi wannan kiran ne a wajen wani taron gangami da su ka kira yau din nan a birnin Yamai

Daruruwan mutanen da su ka halarci gangamin dai na da ra'ayin cewa matukar gwamnatin Kasar ta rage farashin man, rayuwa za ta inganta

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.