BBC navigation

Olusegun Mimiko ya lashe zaben gwamnan jahar Ondo

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:27 GMT
Zabe a Najeriya

Jam'iyyar Labour ta sake lashe zaben jahar Ondo

A Najeriya hukumar zabe a Jahar Ondo dake kudu maso yammacin Kasar ta bayyana sunan gwamna mai ci Mr. Olusegun Mimiko na jam'iyyar Labour, a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan ta shekarar 2012

Jami'in hukumar zaben da ya bayyana sakamakon zaben gwamnan jahar ya ce Mr. Olusegun ya doke abokan karawarsa daga jam'iyyun siyasa 13 da yawan kuri'u dubu dari- biyu da sittin da dari- daya da casa'in da tara.

Tuni dai Shugaban Najeriya Dr. Goodluck Jonathan ya aikewa da zababben gwamnan sakon sa na taya murna.

Sai dai jam'iyyar ACN ta ce akwai rashin tabbas a sakamakon, kuma za ta daukaka kara.

An dai gudanar da zaben gwamnan jahar karkashin tsauraran matakan tsaro.

Sai dai an sami rahotannin sace akwatunan zabe a wasu rumfunan zaben da kuma wsau korafe korafe daga masu kada kuri'a.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.