BBC navigation

Romney ya ce Obama ba shi da ajanda

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 10:51 GMT
obama da romney

'yan takarar shugabancin Amurka Barack Obama da Mitt Romney

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, Mitt Romney, ya yi shagube cewa Barack Obama ba shi da kwakkwarar ajandar sake zama a fadar gwamnatin Amurka ta White House.

Da yake jawabi ga wani gangamin yakin neman zabe a Florida, Romney ya ce gangamin Obama ya tsaya ne a kan wadansu kananan maganganu marasa ma'ana.

Tun da fari Obama ya koka cewa Mista Romney yana ta sauya matsayi yayin da zabe ya ke karatowa. Obama ya zargi dan takarar na jam'iyyar Republican da cewa ya na fama da wata cuta da ya kira ''Romnesia'', wadda a fakaice sunan Mitt Romney ta ke nufi.

Ranar Litinin 'yan takarar biyu za su hadu a muhawararsu ta karshe, a kan manufofin hulda da kasashen waje.

Mista Romney da sauran 'yan jam'iyyar Republican suna ci gaba da mayar da hankali a kan yadda gwamnatin Obama ta tunkari kisan aka yiwa Amurkawa hudu a Benghazi, ciki har da jakadan Amurka a Libya.

Wannan al'amari dai ya janyo ta-da jijiyoyin wuya a muhawarar 'yan takarar ta biyu ranar Talata, kuma mai yiwuwa ne a sake musayar kalamai a kansa a Boca Raton.

'Romnesia'

Mista Obama ya shaidawa magoya bayansa cewa Mitt Romney ya na sassauta matsayinsa ne saboda ganin cewa zabe ya matso kusa.

Obama ya ce: "Ya manta matsayar da ya dauka a baya, sannan kuma yana ganin kamar kuma kun manta''.

Daga nan Obama ya kira yanayin abokin hamayyar tasa da wani suna mai tsuma jama'a wato 'Romnesia'.

Shugaban ya jaddada wa mata masu kada kuri'a cewa ba sa bukatar shugaban da sai ya yi tunani kafin ya nada wasu mata cikin gwamnatisa: "Ba kwa bukatar mutumin da zai nemi a kawo masa takarda cike da sunayen mata", inji Obama, yana gugar zana da yadda Romney ya baiwa mata mukamai lokacin yana gwamnan Massachusetts.

"Kuna bukatar shugaban kasa ne wanda tuni ya nada mata biyu masu ban mamaki a mukaman alkalan Kotun Kolin Amurka".

Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton ma ya fita gangamin nemawa Obama kuri'a a Wisconsin ranar Juma'a.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.