BBC navigation

An kama wasu mutane dangane da sanya wa shugaban kasar Benin guba

An sabunta: 23 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:18 GMT
Shugaban kasar Jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi

Shugaban kasar Jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi

Hukumomi a Jamhuriyar Benin sun kama mutane uku bisa zargin sanyawa Shugaban kasar Thomas Yayi Boni Guba.

Masu gabatar da kara sun ce an kama likitan shugaban Ibrahim Mama Cisse da wata 'yar dan uwa ko 'yar uwar shugaban kasar mai suna Zouberath Koraseke ranar Lahadi, sai dai kuma basu bayyana mutumin da suka kama na cikon ukun ba, Wanda wasu rahotanni ke cewa wani tsohon ministan gwamnatin kasar ne.

Wakilin BBC a Cotonou ya ce an soma zargi akan lamarin ne bayan da shugaban ya fara nuna alamun kasala kuma yana amai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.