BBC navigation

Burtaniya za ta horas da dakarun ECOWAS

An sabunta: 23 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:25 GMT
Sojojin kasar Mali

Sojojin kasar Mali

Burtaniya ta ce za ta iya taimakawa da horo ga sojojin kasashen kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da za'a tura Mali domin kwato yankin Arewacin kasar da ya fada hannun 'yan tawaye a farkon wannan shekarar.

Wakilin musamman na Burtaniya a yankin Yammacin Afruka, Stephen O'Brien ya ce idan ba'a warware rikicin Arewacin kasar ta Mali ba, to akwai yiwuwar a samu mummunar barazanar ta'addanci a Afruka da Turai da ma sauran yankuna.

Mr Obrien ya yi wadannan kalaman ne bayan wata tattaunawa da ya yi a Mali da jami'an gwamnatin kasar da kuma abokan hulda na kasa da kasa.

Makwanni biyu da suka wuce, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya baiwa Shugabannin Afrika kwanaki 45 su tsara wani shiri na daukar matakin soji domin sake kwato arewacin kasar.

Mr O'Brein ya ce a halin yanzu yana dubon zabin taimakon da Birtaniya za ta iya bayarwa.

Ya ce idan ba a mayar da yanci da halaccin Demokuradiyar kasar Mali ba to za a aike da wani sako ga dukanin kungiyoyin yan aware cewar kasashen duniya sun yi watsi da kasashe a cikin kasashe.

Haka kuma ya bayyana damuwa cewar yankin zai iya samar da wani sabon sansani ga hare haren yan ta'adda a Afrika da ma kamar yadda ya ce, daga karshe Turai da ma yankin gabas ta tsakiya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.