BBC navigation

Entwistle ya bayyana a gaban majalisar dokokin Burtaniya

An sabunta: 23 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:20 GMT
Direkta Janar na BBC, George Entwistle

Direkta Janar na BBC, George Entwistle

Darekta Janar na kafar yada labarai ta BBC, George Entwistle, ya musanta cewa shugabanni a BBC ne suka ki amincewa a watsa wani rahoton talabijin akan irin aika-aikar cin zarafin 'yan maata, da ake zargin wani tsohon fitaccen ma'aikacinta ya yi.

Mr Entwistle yana magana ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dokokin birtaniya, dake bincike akan yadda tsohon ma'aikacin BBC, marigayi Jimmy Savile, ya samu sukunin tafka ta'asar da ake zargin shi da aikatawa a tsawon shekaru da dama, ba tare da an tuhume shi ba.

Yanzu dai Editan shirin BBC na Newsnight Peter Rippon ya sauƙa daga kan muƙaminsa yayin da za'a cigaba da bincike a kan wannan lamari.

Tun dai daga lokacin da BBC ta dakatar da watsa rohoton binicke da ya bankaɗo cewa, Jimmy Savile ya yi ta lalata da ƙakanan yara, da cin zarafin mata ta hanyar lalata da su, wasu gidajen talabijin sun watsa shirin dake bayyana zargin lalata da mata da ake yiwa marigayi Jimmy Savile din.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.