BBC navigation

Najeriya: an kama jirgi maƙare da makamai

An sabunta: 23 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:48 GMT

Makamai da aka taɓa kamawa a Najeriya

Sojojin ruwan Najeriya, sun tsare wani jirgin ruwa da matane 15 a cikinsa, wanda galibi 'yan kasar Rasha ne, bisa zargin cewar jirgin na dauke da haramtattun makamai.

Kakakin sojin ruwan ya ce, an samu bindigogi masu sarrafa kansu da dama, da kuma alburusai fiye da dubu takwas a lokacin da jirgin ruwan ya doshi yankin ruwan Legas.

Kamfanin mai jirgin ruwan wato Moran Security Group wanda ofishinsa ke birnin Moscow, ya na samarda kariya daga fashin cikin teku da kuma matsalar yin garkuwa da mutane.

Cikin 'yan shekarun nan dai ana kama jiragen ruwa dauke da makamai da ake kokarin shigarwa Najeriya.

Yanzu haka dai Najeriya tana cikin matsaloli da suka fi ƙamari a yankin arewacin kasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.