BBC navigation

Harin sojojin Isra'ila ya hallaka biyu da raunata wasu da dama

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:55 GMT
Harin yankin Zirin Gaza

Harin yankin Zirin Gaza

Wani hari da sojojin Israela suka kai yankin zirin Gaza ta sama ya kashe 'yan bindigar Hamas akalla biyu ya kuma raunata wasu da dama.

Sojin Israelan sun ce sun kai wa zaratan Hamas din harin ne a dai-dai lokacin da suke kokarin harba makaman roka cikin Israela.

An harba makaman roka din da dama cikin Israela ranar Talata da daddare, wani sojin Israela kuma ya samu rauni sakamakon wata fashewa akan iyaka.

Israelan ta kai harin ne sa'oi kadan bayan da sarkin Qatar ya bar Gaza bayan ziyarar da ya kai wadda ita ce ta farko da wani shugaba na wata kasar waje ya kai yankin tun lokacin da Hamas ta kama mulki shekaru biyar da suka wuce.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.