BBC navigation

Darakta Janar na BBC ya musanta zargin kin watsa wani rahoto

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:29 GMT
George Entwistle Darakta Janar na BBC

George Entwistle Darakta Janar na BBC

Darakta Janar na kafar yada labarai ta BBC, George Entwistle, ya musanta cewa shugabanni a BBC ne suka ki amincewa a watsa wani rahoton talabijin akan irin aika-aikar cin lalata da 'yan mata, da ake zargin wani tsohon ma'aikacinta Jimmy Savile ya yi.

Mr Entwistle na bayyana hakan ne lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dokokin Birtaniya dake bincike kan yadda tsohon ma'aikacin BBC, marigayi Jimmy Savile ya samu sukunin tafka ta'asar da ake zargin aikatawa a tsawon shekaru da dama ba tare da an tuhume shi ba.

An dai zargi BBC ne da jingine binciken tsohon ma'aikacin nata Jimmiy Savile ne saboda tana wani shiri na watsa shirye-shirye kan girmama shi.

A lokacin da yake amsa tambayoyin kwamitin majalisar, daya daga cikin 'yan majalisar ya zargi Mr Entwistle da nuna halin ko in kula, inda ya gaza kara bincikawa lokacin da aka fara shaida masa cewa manema labarai na gudanar da bincike kan marigayi mai gabatar da shirye-shiryen.

Mr Entwistle din dai ya shaida wa 'yan majalisar cewa a wancan lokacin yana rike da mukamin shugaban sashen watsa shirye-shiryen talabijin da bashi da alaka da yada labarai ne saboda haka shi yasa bai iya maida hankali sosai kan matakan da ya kamata a ce manajojin sashen labarai sun dauka ba.

Sakatariyar harkokin al'adu ta Birtaniya, Maria Miller dai ta ce wannan abin fallasa ya haifar da matukar damuwa game da batun amincewar jama'a ga BBC.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.