BBC navigation

An cimma yarjejeniya a Syria

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:51 GMT
Lakhdar Brahimi

Wakilin MDD a Syria

Wakilin majalisar dinkin duniya a Syria, Lakhdar Brahimi, ya ce gwamnatin Syria da wasu kungiyoyin mayakan 'yan tawaye sun amince su tsagaita bude wuta lokacin bukuwan babbar Sallah.


Amma duk da haka, ma'aikatar harkokin wajen Syria, ta ce sojojin kasar na nazari a kan bukatar, kuma za ta sanar da shawarar da ta yanke a gobe.

Mista Brahimi wanda ke shiga tsakani a rikicin, ya ce tsagaita wutar za ta fara aiki ne a ranar Juma'a har zuwa kwanaki hudu dake tafe.


Sai dai kuma kakakin 'yan tawaye na Free Syrian Army, Loay Al Moqdad ya gindaya wasu sharuda.

Yayinda ake kokarin kulla wannan yarjejeniya, wani babban kwamandan dakarun Rasha ya ce yan tawayen kasar ta Syria sun samu makamai masu linzami, wasu daga ciki kirar Amurka.


Janar Nikolai Makarov ya ce babu tabbas kan inda suka samu makaman kirar Amurka, amma ya kamata a gudanar da bincike.


Amurka dai ta musanta bada makamai ga 'yan tawayen.

Rasha dai itace kan wajen wajen samar da makamai ga gwamnatin Syria.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.