BBC navigation

Ana tallafawa kungiyoyin dake dauke da makamai da kudaden zinare a Congo

An sabunta: 25 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:08 GMT
'Yan tawayen Congo

sayar da zinare wajen tallafawa 'yan tawaye

Rahotan da wata Kungiya kamun kafa a Amurka ta fitar yace zinaren da ake fasakauri ya kasance wata hanya mai tsoka da ake amfani da ita wajen samun kudaden tallafawa kungiyoyin dake dauke da makamai a gabashin damukradiyar jamhuriyar Congo

Kungiyar wacce ake kira Enough tace idan aka kwantata zinaren da sauran albarkatun kasa, yana da sauki ayi fasakaurin sa akan iyakokin Congo domin a sayar da shi a kasashen duniya

Wakilin BBC yace Kungiyar tana neman masu sayayya dasu matsawa masu saida shi lamba, na kada su yi amfani da duk zinaren da ya fito daga kasar Congon

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.