BBC navigation

Uganda za ta dakatar da shiga tsakani a wasu kasashen Afirka

An sabunta: 25 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:29 GMT
Taswirar kasar Uganda

Taswirar kasar Uganda

Kasar Uganda ta ce mai yiwuwa ta dakatar da ayyukan shiga tsakani da wanzar da zaman lafiya a wasu sassan kasashen Afirka masu fama da rikici, bayan da rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya soki ayyukanta a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Majalisar Dinkin Duniyar dai ta zargi kasar Ugandar da marawa 'yan tawaye baya.

Wani minista a gwamnatin ta kasar Uganda, Asuman Kiyingi ya shaidawa BBC cewa batun da ake cewa kasar Uganda na marawa 'yan tawaye baya a taron tattaunawa kan zaman lafiya wani yarfe ne, kuma ya bata kimar Ugandar.

Ministan yace an yi mummnuar bata sunan Uganda sakamakon abinda ya kira yarfe, kuma ba za su lamunta ba.

Yace kuma ce ta yiwu Uganda za ta janye ayyukanta daga yankunan dana daukacin nahiyar.

Mr Kiyingin ya kuma kara da cewa idan dai ba an janye wannan zargi ba, kana aka yaba da gudummawar da kasarsa ta taka, gwamnatin sa zata janye jami'an shiga tsakaninta da ma dakarunta da yanzu haka ke gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya karkashin Majalisar Dinkin Duniya a kasashen Somalia da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.