BBC navigation

Dan kunar bakin wake a Afghanistan ya hallaka mutum 40 a hari kan masallaci

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:47 GMT
Hari a Afghanistan

Dan kunar bakin wake ya hallaka jama'a a masallaci

Wani dan kunar bakin wake ya kai hari akan wani masallaci dake arewacin Afghanistan, inda ya kashe mutane arba'in da daya ya kuma raunata fiye da mutane hamsin.

Yawancin wadanda lamarin ya rusta da su 'yan sanda ne.

Dan kunar bakin waken ya samu nasarar wucewa ta shingayen bincike har hudu kafin ya kai kofar masallacin dake garin Maymana, kuma ana zaton cewar yana sanye ne da kayan 'yan sanda.

Gwamnan lardin da wasu manyan jami'an gwamnati duk su na wajen, amma ana tunanin babu abinda ya same su.

Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai ya bukaci masu ta'asa su yi hakuri.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.