BBC navigation

Isra'ila ta zargi kasar Sudan da marawa kasar Iran baya

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:29 GMT
Firai Ministan Isra'ila Bebjamin Netanyahu

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Manyan jami'an gwamnatin Israela sun zargi Sudan da cewa itace cibiyar da Iran ke amfani da ita wajen aikawa masu gwagwarmaya da makamai a Afrika da gabas ta tsakiya makamai.

Mataimakin Frai Ministan Israela Moshe Yaalon ya bayyana Sudan da cewa matattara ce ta yada ta'addanci.

Wadannan kalaman na zuwa ne bayan da Sudan ta zargi Israela da kai harin da ya haddasa fashe-fashe a wata masana'antarta ta makamai a Khartoun, da ta ce Israelan ce ta kai mata hari ta sama,

Wanda kuma a kan hakan Sudan tace zata gabatar da korafinta ga kwamitin tsaro na majalisar Dinkin Duniya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.